Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan kusoshin kasashe daban daban sun yarda da kafuwar dokar tsaron kasa da ta shafi Hong Kong
2020-06-30 20:03:40        cri

Manyan kusoshin kasashen Afirka ta kudu da Madagascar da Iran da kuma Nepal, sun bayyana amincewarsu da yadda majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta kafa dokar tsaron kasa da ta shafi yankin Hong Kong na kasar, manufar da ta shafi tabbatar da tsaron kasa, don haka ba wani kuskure a ciki.

Solly Mapaila, shi ne mataimakin babban sakatare na biyu na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Afirka ta Kudu, ya bayyana cikakken goyon bayansa kan kafuwar dokar tsaron kasa da ta shafi Hong Kong, ya kuma ce jam'iyyarsa tana Allah wadai da munanan aikace-aikacen masu tada zaune-tsaye a yankin Hong Kong, da yunkurin balle yankin daga kasar Sin.

A nasa bangaren, shehun malami a jami'ar Toamasina ta kasar Madagascar Solofo Randrianja, ya ce kafuwar dokar tsaron kasa mai alaka da yankin Hong Kong, za ta taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki a yankin, da sanya manufar "Kasa daya amma tsarin mulki biyu" ta dore. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China