Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani: Dokar da kasar Amurka ta zartas kan batun Hong Kong ta sabawa ka'idojin kasa da kasa
2020-06-28 16:53:15        cri

Wani shahararren masani mai nazarin al'amuran duniya da harkokin siyasa na kasar Pakistan, Fayaz Kiyani, ya bayyana wa wakilin CRI a jiya Asabar cewa, yadda kasar Amurka ke tsoma baki cikin batun da ya shafi yankin Hong Kong na kasar Sin, ya lahanta moriyar kasar Sin, da ta jama'ar yankin Hong Hong, kuma ya keta ka'idojin kasa da kasa.

A cewar mista Fayaz, duk da cewa kasar Amurka ta ki yarda da dokar tsaron kasa da ake neman kafawa a yankin Hong Kong, amma hakika Amurka ita kanta na da dokar tsaron kasa a gidanta, batun da ya nuna cewar kasar ba ta da adalci ko kadan, wadda ke raba kafa a fannin ra'ayinta na tabbatar da tsaron kasa.

Ban da haka, masanin ya kara da cewa, dokar tsaron kasa da kasar Sin ke neman kafawa a yankin Hong Kong ta dace da yanayin da yankin ke ciki, domin ana ta samun al'amura masu ta da hankali a yankin, sakamakon rashin wannan doka. Saboda haka, kafuwar dokar ta zama wajibi, bisa la'akari da yadda za ta dinke barakar rarrabuwar kawunan jama'ar yankin, da yunkurin bata yanayin da ake ciki na samun walwala da kwanciyar hankali a yankin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China