Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta mayar da martani ga yunkurin kasar Amurka na sanya mata takunkumi
2020-06-30 20:02:10        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya furta a yau Talata a birnin Beijing hedkwatar kasar Sin cewa, batun kafa dokar tsaron kasa da ta shafi yankin Hong Kong, harka ce ta cikin gidan kasar Sin, saboda haka babu ruwan sauran kasashe da batun. Sa'an nan dangane da matakin takunkumi da kasar Amurka ke shirin dauka, kasar Sin za ta mayar da martani da wasu matakai, don tabbatar da kare moriyar ta.

A jiya Litinin, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ya ce kasarsa za ta dakatar da sayar da kayayyakin tsaron kasa ga yankin Hong Kong na kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China