Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Watalika Lokacin Barkewar Cutar COVID-19 A Wasu Kasashe Ya Riga Lokacin Da Aka Sanar
2020-06-28 20:48:05        cri

Jaridar Ta Kung Pao ta yankin Hongkong na kasar Sin ta ba da labari a yau Lahadi cewa, bayan an yi nazari mai zurfi kan cutar COVID-19, hakikanin lokacin barkewar cutar a wasu kasashe ya canja, an ce, watakila barkewar wannan cuta ko yaduwar cutar a cikin wasu kasashe ya riga lokacin da aka sanar a baya.

Ranar 15 ga watan Mayu, ministan kiwon lafiya da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a Kato Katsunobu ya nuna cewa, kungiyar Red Cross ta kasar ta gano cewa, samfurin jinin mutane biyu ya bayyana alamar kamuwa da cutar daga cikin samfurorin jini guda 500 da aka tattara a farkon shekarar bara.

Ban da wannan kuma, ranar 26 ga watan Yuni, masanan kwayoyin cuta na kasar Spaniya sun gano kwayar cutar a cikin gurbataccen ruwa na watan Maris na shekarar 2019, lokacin da ya zarce sanarwar bullar cutar da watanni 9.

Dadin dadawa, asibitin Albert Schweitzer na birnin Colmar na kasar Faransa ya ba da sanarwa a ranar 7 ga watan Mayu cewa, daga cikin marasa lafiya dake cikin asibitin, akwai wanda ake zaton ya kamu da cutar a ranar 16 ga watan Nuwambar bara.

Game da asalin cutar, daktan jam'iyyar Cambridge Peter Forster ya bayyana ra'ayinsa cewa, ya zuwa yanzu babu hakikanin amsa kan wannan tambaya, amma a cewarsa, bisa nazarin da aka yi, mai yiwuwa ne wannan cuta ta harbi mutane tun daga ranar 13 ga watan Satumba zuwa ranar 7 ga watan Disamba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China