![]() |
|
2020-05-10 16:41:58 cri |
Mambobin kasashen kwamitin sulhun MDD sun amince da daftarin bayanai bisa ga kokarin da kasashen Faransa da Tunisia suka nuna. Kasar Sin ta goyi bayan kudurin. Amurka ma ta nuna goyon bayanta.
Sai dai abin mamaki da takaici, Amurka ta canza matsayinta, lamarin da ya sa kwamitin sulhun MDD ta kasa samun damar zartar da kudurin. Jakadan kasar Sin ya ce, Amurka tana kawo koma baya wajen hadin kan kwamitin sulhun MDD, kuma tilas ne ta dauki alhakin wannan batu a wannan rana.
Ya ce kasar Sin ta nuna cikakkiyar amincewa, kuma za ta ci gaba da goyon bayan wannan kuduri. Kasar Sin tana goyon bayan matakin kwamitin sulhun MDD game da bukatar da babban sakataren MDD ya nuna kan batun tsakaita bude wuta a kasa da kasa, da bunkasa aikin jin kan bil Adama da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaron dakarun wanzar da zaman lafiyar MDD.
Wakilin na kasar Sin ya ce, Sin tana goyon bayan kudurin da ya shafi rawar da hukumar lafiya ta duniya WHO ke takawa wajen aikin yaki da annobar COVID-19, wajen samar da muhimmin tallafin kiwon lafiya.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China