![]() |
|
2020-06-04 10:15:13 cri |
Bayan nazartar sama da sakonnin Tiwita miliyan 2.6 da cibiyar ta tattara cikin kwanaki goma na karshen watan Maris, sakamakon binciken ya nuna cewa, wadannan kungiyoyi masu amfani da shafin Tiwita 28 dake da nasaba da 'yan siyasa masu ra'ayin rikau ko QAnon, su ne suka yada labari kan asalin cutar COVID-19.
Wata kafar yada labaran 'yan siyasar Amurka mai suna Politico, ta sanar a ranar Talata cewa, tun a farkon watan Janairun wannan shekara, ake ta yada jita-jita a kafafen sada zumunta game da cutar cewa, wasu gwamnatocin kasashe sun kirkiri sabuwar kwayar cuta, don gwada karfinsu na soja. Sai dai hukumar lafiya ta duniya da sauran kungiyoyi masu bibiyar bayanai, sun yi watsi da wannan jita-jita.
Rahoton ya kara da cewa, masu binciken sun gano cewa, wadannan kungiyoyi masu amfani da shafin Tiwita, sun raba jita-jita game da, wai COVID-19, wani makamai mai guba ne da kasar Sin ta kirkiro sau kimanin 900.
A farkon watan Mayu ma, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce, yana da kwakkwarar shaidar dake nuna cewa, kwayar cutar ta samo asali ne daga birnin Wuhan dake yankin tsakiyar kasar Sin, sai dai bai ba da wata shaida da za ta gaskata ikirarin nasa ba.
A hannu guda kuma, hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, irin wannan ikirari game da asalin cutar, jita-jita ce kawai, domin hukumar ba ta samu wasu bayanai ko shaidu kan wannan batu daga bangaren Amurka ba. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China