![]() |
|
2020-06-26 10:54:34 cri |
Kayayyakin sun hada da abin wanke hannu guda 100 da sabulun wanke hannu lita 550 wadanda aka kiyasta kudinsu kimanin shillings miliyan 22 na kudin Tanzania kwatankwacin dala 9,500.
Gudunmawar, aiki ne na hadin gwiwa wanda ya kunshi hukumomin shiyyar Dar es Salaam da gidauniyar SukosKova, kuma za'a aika kayayyakin zuwa makarantun yankin gabanin bude makarun kasar da ake sa ran bude su a ranar 29 ga watan Yuni.
Wang Ke, jakadan Sin a kasar Tanzania, ya ce tun bayan barkewar annobar COVID-19, kasar Sin ta samar da tallafin kayayyakin yaki da annobar ga kasar Tanzania, kuma an sha shirya tarukan karawa juna sani ta kafar bidiyo sau da dama inda kwararrun masana kiwon lafiya na kasar Sin da Tanzaniya suka yi musayar kwarewa don yaki da annobar, da aikin binciken masu fama da cutar, da ba su kulawa, wanda ya kunshi har da yin amfani da magungunan gargajiya don kula da masu dauke da cutar ta COVID-19.
Lawrence Malangwa, sakataren mulki na shiyyar Dar es Salaam, ya godewa ofishin jakadancin kasar Sin, inda ya bayyana cewa gudunmawar ta kara bayyana matsayin dadaddiyar dangantakar dake tsakanin Sin da Tanzaniya. (Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China