Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WTO ta jaddada muhimmancin auduga ga kasashe masu tasowa
2019-10-08 12:33:21        cri

Darakta Janar na kungiyar kula da cinikayya ta duniya WTO, Roberto Azevedo, ya jaddada muhimmancin auduga ga kasashe masu tasowa da dama.

Roberto Azevedo ya bayyana haka ne jiya a birnin Geneva, yayin kaddamar da ranar auduga ta duniya na farko, wadda ke da nufin hada noma da cinikayyar auduga domin kara darajarsa a kasashe masu tasowa.

Yayin wani taron musammam na ministocin kasashe mambobin kungiyar, an bayyana muhimmancin auduga ga kasashen dake nomansa kamar Benin da Burkina Faso da Chadi da Mali da ake kira da C4, da sauran kasashe masu tasowa da matalautan kasashe.

A cewar Zhang Xiangchen, wakilin Sin a WTO, a matsayin kasar Sin na kasar da tafi kowacce samarwa da amfani da auduga, ta bada gagarumar gudunmuwa ga raya masana'antar auduga na duniya.

Ya ce samar da auduga wani bangare ne dake habaka dangantakar Sin da Afrika, yana mai ba da misali da wasu ayyukan da Sin ta tallafawa a nahiyar, da suka hada da Cibiyar horar da fasahohin aikin gona ta Chadi da kamfanin masaka na Benin da kuma masakar Segou ta Mali.

Ya ce yayin da auduga ke da muhimmanci kuma ya kasance bangaren aikin gona da kasashe 4 masu samar da shi suka fi ba muhimmanci, kasar Sin za ta bada muhimmanci ga yarjeniyoyin da suka shafi auduga, da ci gaba da taka muhimmiyar rawa da hada hannu da sauran mambobin WTO da nufin samun sakamako mai kyau a bangaren. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China