Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hakika Amurka ba za ta yi nasara ba idan ta ci gaba da fakewa da batun Xinjiang don tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin
2020-06-19 20:41:23        cri
Jiya Alhamis, kafar talabijin ta kasa da kasa ta kasar Sin CGTN ta bullo da wani sabon shirin TV cikin harshen turanci mai suna "Tianshan: Still Standing - Memories of Fighting Terrorism in Xinjiang 2020", wato tunawa da yadda ake kokarin yakar ta'addanci a Xinjiang. A ranar ce kuma, Amurka ta sa hannu kan shirin dokar kare hakkin dan Adam na Uygur na shekara ta 2020.

Game da batun, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian ya jaddada cewa, batun jihar Xinjiang ba shi da alaka ko kadan da hakkin dan Adam, ko wata kabila, ko kuma wani addini, amma batu ne da ya jibanci yaki da ta'addanci da masu kawowa kasar Sin baraka. Wannan sabon shirin TV ya gabatar da kwararan shaidun dake bayyana wajibcin yaki da ta'addanci da kawar da masu tsattsauran ra'ayi a Xinjiang, da nuna namijin kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi a wannan fanni.

Har wa yau, Zhao ya ce, matakan da gwamnatin Xinjiang ta dauka sun dace da doka, wadanda suka taka birki sosai ga aukuwar ayyukan ta'addanci a wurin. Kuma ba'a samu faruwar aikin ta'addanci ko sau daya ba a cikin shekaru uku da rabi a jere a Xinjiang, al'amarin da ya tabbatar da hakkokin tsaro da lafiya da ci gaba na al'ummomi daban-daban a wurin. Hakazalika kuma, kasashen duniya sun jinjinawa gwamnatin kasar Sin saboda managartan manufofinta kan jihar.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China