2020-06-02 10:11:25 cri |
Wata sanarwar da aka fitar bayan kammala wani taron manema labarai a jiya Litinin, ta bayyana cewa, yankin na Xinjiang, ya zuba kudade masu tarin yawa a fannin gine-gine da gyara da fadada makarantun reno kimanin 4,408 a yankunan karkarar yankin.
Bayanai na nuna cewa, yanzu haka dukkan yara masu shekaru 4 zuwa 6 da suka isa shiga makarantun reno a yankin mai cin gashin kansa, suna samun ilimi a irin wadannan makarantun reno, baya ga abincin rana da 'ya'yan itatuwa da kayan ciye-ciye da ake ba su kyauta.
Hukumomin yankin sun bayyana cewa, a shekarar 2019, yankin na Xinjiang ya kashe Yuan biliyan 86.31 a fannin ilimi, karuwar kimanin Yuan biliyan 4.77 ko kaso 5.85 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China