Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xinjiang tana kara inganta tsarin kiwo lafiya
2020-06-03 16:01:57        cri

Darektan kwamitin kiwo lafiya na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, Mutellip ya bayyana a kwanan baya cewa, jihar tana mai da hankali matuka kan lafiyar jama'ar wurin, da kuma kara inganta tsarin kiwon lafiya.

Kwanan baya, kungiyar ta'addanci ta gabashin Turkistan dake ketare wato "East Turkistan" ta yi ikirari cewa, cibiyar koyar da sana'o'i na fuskantar kalubalen yaduwar COVID-19, Mutellip ya mai da martani cewa, daliban cibiyar sun kammala karatunsu tun a farkon watan Disamba na bara, to yaya za a samu barazanar yaduwar cutar a cibiyar? Rahotanni na cewa, ba a samu sabon rahoton wanda ya kamu da cutar a jihar a cikin kwanaki 100 a jere ba, abin da ya sa aka farfado da harkokin rayuwa na yau da kullum a duk fannoni a jihar.

Ban da wannan kuma, darektan kula da harkokin kabilu na jihar ya ce, kungiyar "East Turkistan" ta yada jita-jita wai an hana musulmi a jihar yin azumi, ba gaskiya ba ne (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China