Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin MDD ya bukaci Amurka da ta rungumi ka'idojin kasa da kasa don yaki da wariyar launin fata
2020-06-16 12:53:48        cri

Kwamitin MDD mai rajin yaki da nuna wariya, ya bukaci kasar Amurka da ta rungumi ka'idojin kasa da kasa don yaki da wariyar launin fata, ta hanyar gaggauta sauya tsare tsare, da sauke nauyin dake wuyanta, karkashin tanade-tanaden da aka amince da su.

Cikin wata sanarwa a hukumance, wadda aka wallafa a jiya Litinin, kwamitin ya yi kira ga mahukuntan Amurka, da su martaba dokar kasa da kasa mai nasaba da wannan batu, wadda Amurkan ta rattabawa hannu a shekarar 1994, su kuma kara horas da jami'an tsaro, game da tanaje tanajen dokar.

Kwamitin mai kunshe da kwararru 18 masu zaman kansu, ya nuna damuwa game da kisan bakar fatar nan wato George Floyd, wanda wani dan sanda ya hallaka a Minneapolis, da ma kisan Amurkawa bakaken fata da dama da 'yan sanda, da sauran mutane ke aikatawa a kasar cikin shekaru da yawa da suka wuce.

Kaza lika kwamitin, ya kuma bukaci gwamnatin Amurka da ta bayyana irin tanadin da take da shi, game da matakan yaki da wariyar launin fata a tsakanin al'ummar kasar, ta kuma fayyace adawar da yake yiwa kisan bakaken fata, da sauran al'ummu marasa rinjaye. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China