Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An canja matsayin hukuncin kisan da aka yiwa dan sanda dake hannu a mutuwar George Floyd
2020-06-04 11:15:37        cri
Masu gabatar da kara a kasar Amurka a jiya Laraba, sun daga matsayin hukuncin da aka yanke wa tsohon jami'in dan sandan Minneapolis mai suna Derek Chauvin da aka kora daga aiki, bisa zargin danne wuyan George Floyd da gwiwar kafarsa, zuwa hukuncin kisa ba da gangan ba.

An kuma yankewa sauran jami'an 'yan sanda uku dake da hannu a mutuwar Floyd hukunci, saboda taimakawa da suka yi har ya kai ga mutuwar Floyd.

Babban lauyan jihar Minnesota Keith Ellison, ya sanar a taron manema labarai cewa, an yanke wa dan sandan da aka kora daga aiki, kuma yake hannu wato Derek Chauvin, hukuncin kisa ba da gangan ba daga hukuncin sanadin kisa da aka yanke masa a baya.

Ellison ya kara da cewa, ba za su yi gaggawa wajen yanke hukunci ba, saboda batu ne mai wahalar gaske wadda ke bukatar tsage gaskiya. A don haka, gabanin kaiwa ga haka, ya bukaci shugabanni a dukkan matakai na gwamnati gami da daukacin 'yan kasar, da su fara sake rubuta dokokin da za su dace da al'ummar da muke ciki. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China