Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu adalci cikin matakan da yan sandan Amurka ke aiwatarwa kan yan asalin Afirka
2020-06-08 13:49:05        cri

A ranar 5 ga wannan wata, an canja sunan titin dake gaban fadar White Housa dake birnin Washington na Amurka, zuwa "Rayuwar bakaken fata ita ma rayuwa ce". Kana magajin birnin, ya bada umurnin rubuta sabon sunan a kan titin da launin rawaye, don nuna goyon baya ga manufar kiyaye hakkin dan Adam na 'yan asalin Afirka.

A kwanakin nan, sau da dama jama'a daga wurare daban daban na kasar Amurka, suna ci gaba da zanga-zanga, don nuna adawa da amfani da karfin tuwo da 'yan sanda suke yi, da kuma rashin adalci ga kabilu daban daban, da kuma bukatar sake yin tunani game da wadannan batutuwa dake faruwa a dogon lokaci a kasar Amurka.

Masu zanga zangar na cewa matsalar nuna karfin tuwo ga Amurkawa 'yan asalin Afirka na kara tsananta, ana kuma kara gabatar da kididdigar yawan nuna karfin tuwo ga 'yan asalin Afirka a kasar.

Da farko dai, 'yan asalin Afirka su ne wadanda suka fi fuskantar matsalar nuna musu karfin tuwo daga bangaren 'yan sanda. Bisa labarin da jaridar The New York Times ta bayar, a birnin Minneapolis, inda yawan 'yan asalin Afirka bai kai kashi 20 cikin dari, cikin jimillar adadin mutanen dake birnin, kasha 60 cikin dari na yawan mutanen da 'yan sanda suka nunawa karfin tuwo 'yan asalin Afirka ne.

Tun daga shekarar 2015, an lissafa matakin 'yan sanda na amfani da karfin tuwo guda 11,500 a birnin, a cikin guda 6,650 ya shafi 'yan asalin Afirka ne.

Na biyu, yawan 'yan asalin Afirka da 'yan sanda suke nunawa karfin tuwo, ya fi na fararen fata sosai. Bisa labarin da jaridar The New York Times ta bayar, a cikin ayyukan yin kashedi tare da bindiga guda 171 da 'yan sanda suka yi a birnin Minneapolis, 'yan asalin Afirka sun fuskanci kaso 68 cikin dari cikin jimillar adadinsu. Kana a cikin ayyukan yin kashedi ta amfani da abubuwan guba guda 1748, 'yan asalin Afirka sun fuskanci kashi 66 cikin dari. Hakan yake a cikin sauran hanyoyin yin kashedi na karfin tuwo. Kaza lika hakan ya shaida cewa, fiye da rabin yawan mutanen da 'yan sanda suka nunawa karfin tuwo 'yan asalin Afirka ne.

Na uku, dalilin da ya sa matsalar ta fito fili shi ne, rashin yanke hukunci mai karfi ga masu amfani da karfin tuwo. Tun daga shekarar 2012, an hori masu laifi 'yan sanda 15 ne kacal, cikin korafi fiye da 2600 da aka gabatar kan 'yan sandan birnin Minneapolis, kuma hukunci mafi tsanani da aka yi musu shi ne dakatar da su daga aiki har na tsawon awoyi 40 kacal.

Forfesa Keith, mai kula da harkokin 'yan asalin Afirka da nahiyar Afirka, na jami'ar Minnesota ya bayyana cewa, ba a nuna adalci ga al'umma a zamantakewar al'ummar kasar Amurka, kuma a kan nuna rashin daidaito ga 'yan asalin Afirka. Ya ce idan an ci gaba da fuskantar irin wannan matsala, ba za a samu hakikakin adalci a kasar Amurka ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China