Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kashe sama da yuan triliyan 5 a kan ilimi a shekarar 2019
2020-06-16 10:33:45        cri

Ma'aikatar ilimi ta kasar Sin, ta ce kasar ta kashe kimanin yuan triliyan 5.01, kwatankwacin dala biliyan 706.6, a kan ilimi a fadin kasar a shekarar 2019, wanda ya karu da kaso 8.74 a kan na shekarar da ta gabace ta.

Rahoton da ma'aikatar ta fitar, ya nuna cewa kasafin kudin da gwamnati ta kashe kan ilimi ya kai sama da yuan triliyan 4 a baran, wanda ya karu da kaso 8.25 kan na shekarar 2018.

Rahoton ya kara da cewa, a shekarar 2019, an kashe sama da yuan triliyan 2.2 a kan tsarin ilimin dole, adadin da ya karu da kaso 9.12 da kuma sama da yuan triliyan 1.3 kan ilimin gaba da sakandare, wanda ya karu da kaso 11.99 a kan na shekarar 2018. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China