Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoton UNESCO ya yabawa kokarin kasar Sin game da ilmin manya
2019-12-06 11:05:01        cri

Wani rahoton kasa da kasa karo na hudu game da ilmin manya wato (GRALE) a takaice, wanda aka wallafa a ranar Alhamis a helkwatar hukumar kula da ilmin kimiyya da raya al'adu ta MDD UNESCO a birnin Brussels, ya yi maraba da namijin kokarin da kasar Sin ke yi wajen ilmantar da manya masu yawan shekaru da yadda kasar ke taimakawa ilminsu, lafiyarsu, har ma da yanayin zaman rayuwarsu.

Bisa ga alkaluman da mambobin kasashe 159 suka mikawa UNESCO, rahoton ya ce, kasar Sin tana ware sama da kashi 4 bisa 100 na kasafin kudinta wajen ilmin manya, kuma ita ce kasa 1 tilo cikin kasashe 13 na duniya da suke baiwa wadannan rukunin al'umma muhimmancin da ya dace.

Rahoton ya ce, kasar Sin ta kafa jami'o'i da makarantu ga tsoffi a matakan larduna, da kananan hukumomi, da yankuna wato gundumomi, kuma an samu gagarumin ci gaba wajen raya ci gaban ilmin manya a yankunan kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China