Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Guinea Bissau ya rusa gwamnatin kasar gabanin zaben shugaban kasa
2019-10-29 13:46:15        cri

Shugaban kasar Guinea Bissau Jose Mario Vaz, ya rusa gwamnatin kasar dake karkashin Firaminista Aristides Gomes, bisa wani umarnin Shugaban kasa, sai dai Firaminista Gomes, ya ki amincewa da matakin.

An fitar da umarnin ne bayan taron majalisar gudanarwar kasar, wadda ke ba da shawara ga shugaban kasa.

Sai dai, Firaministan ya ce ba zai girmama matakin na Shugaban da bai cancanta ba.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta yi gargadi kan rusa gwamnatin kasar kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba.

Tun daga shekarar 2015 Guinea Bissau ke fama da rikicin siyasa, a lokacin da shugaba Vaz ya kori Firaminista Domingos Simoes Pereira na wancan lokaci, wanda ya kasance babban abokin hammayarsa.

Zaben shugaban kasar na bana zai gudana ne a ranar 24 ga watan Nuwamba, kuma aka shirya gudanar da zagaye na 2 a ranar 29 ga watan Disamba, idan babu wanda ya samu sama da kaso 50 na kuri'un da aka kada a zagaye na farko. (Fa'izaMustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China