Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU zata sanya ido don duba ingancin zaben shugaban kasar Guinea Bissau
2019-12-28 17:23:08        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sanar a ranar Juma'a cewa a shirye take ta sanya ido don tabbatar da ingancin zaben shugaban kasar Guinea Bissau dake tafe, wanda za'a gudanar a gobe ranar 29 ga wata.

Tawagar jami'an sa idon na kungiyar tarayyar Afrika a zaben wato AUEOM a takaice, ta riga ta isa kasar Guinea Bissau tun a ranar 22 ga watan Disambar 2019, zata duba tare kuma da auna ingancin zaben shugaban kasar na ranar 29 ga watan Disamba, da nufin bayar da gudunmowa wajen tabbatar da yin zaben cikin kwanciyar hankali, da sahihanci da kuma inganci, kungiyar mai mambobi kasashen Afrika 55 ta bayyana cikin sanarwar a ranar Juma'a.

Haka zalika kungiyar ta kasashen Afrika ta sanar da isar tsohon firaministan Sao Tome da Principe, Joaquim Raphael Branco, zuwa Bissau, babban birnin kasar ta Guinea Bissau a matsayin shugaban tawagar masu sanya ido na kungiyar AU a zaben.

AU ta kara da cewa, aikin tawagar sanya idon da aka tura Guinea Bissau tun a ranar Juma'a, zai shafi dukkan shiyyoyi 9 dake Guinea Bissau, a yayin da ake shirin kammala gangamin yakin neman zaben kasar da kuma shirye shiryen zuwan ranar jefa kuri'ar a kasar.

A ranar 27 ga watan Nuwamba, hukumar zaben kasar Guinea-Bissau ta sanar da cewa za'a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a ranar 29 ga watan Disamba, bayan da tsoffin firaministocin kasar biyu wato Domingos Simoes Pereira da Umaro Sissoco Embalo suka samu kashi 40.13 da kashi 27.65 bisa 100 na kuri'un da aka kada a zagayen farko na zaben shugabancin kasar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China