Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon sakataren tsaron Amurka: da gangan Trump ya ke dasa rabuwar kai tsakanin Amurkawa
2020-06-04 14:09:35        cri

Tsohon sakataren tsaron Amurka, Jim Mattis, ya yi tsokaci yayin da ake fama da rashin kwanciyar hankali a Amurka, inda ya ce, shugaban kasar Donald Trump, na kokarin raba kan Amurkawa.

Cikin wani sharhinsa da mujallar the Atlantic ta wallafa, Jim Mattis ya ce tsawon rayuwarsa, Donald Trump ne shugaban kasar na farko da bai yi wani kokari na hada kan al'ummar Amurkawa ba, yana mai cewa ko kokarin hakan ba ya yi.

Ya ce yanzu ana ganin sakamakon halin-ko-in-kula da ya nuna cikin shekaru 3. Haka kuma ana shaida sakamakon shugabanci mara kan gado da ya shafe shekaru 3 yana yi.

Jim Mattis, tsohon Janar na rundunar sojin ruwan Amurka ne da ya yi murabus daga mukaminsa na sakataren tsoron kasar a watan Disamban 2018, bisa adawa da manufar shugaba Trump dangane da batun Syra. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China