Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnan Minnesota ya yi kira da a binciki ofishin 'yan sandan jihar kan laifin take hakkin bil-Adama
2020-06-03 10:18:33        cri

Gwamnan jihar Minnesato Tim Walz, ya bayyana a jiya Talata cewa, jiharsa za ta kaddamar da bincike kan zargin take hakkin bil-Adama da ake yiwa ofishin 'yan sandan jihar (MPD) da aikatawa, inda ake zargin wasu jami'anta hudu da hannu a kisan wani bakar fata mai suna George Floyd a makon da ya gabata.

Walz ya bayyana cewa, ofishin kare hakkin bil-Adama na jihar, ya shigar da kara kan zargin take hakkin bil-Adama da ake yiwa ofishin 'yan sandan jihar, kana zai binciki manufofi da dabaru da ayyukan da ofishin ya gudanar cikin shekaru 30 da suka gabata, don gano ko an yi amfani da ayyukan dake da alaka na nuna wariya.

Gwamnan wanda ya bayyana haka cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, bayan kammala taron manema labarai, Ya jaddada cewa, gwamnatinsa za ta yi amfani da dukkan matakan da suka wajaba, don ganin an kawar da ayyukan nuna wariyar launin fata a jihar. Yana mai cewa, wannan na daga cikin matakan da za a dauka, a kokarin da gwamnatinsa ke yi na dawo da yarda da amince tsakanin al'ummomin da suka bace ba a sake jin rudiyarsu ba na tsawon lokaci.

A ranar 25 ga watan Mayu ne dai, Floyd ya gamu da ajalinsa, bayan da jami'an 'yan sandan jihar suka danne wuyansa da gwiwar kafa, bayan an kama shi bisa zarginsa da sayen taba sigari da jebun dala ashirin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China