![]() |
|
2020-06-04 11:37:02 cri |
A wata sanarwa da aka baiwa kwafenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kakakin rundunar sojojin John Enenche ya ce, farmakin da sojojin suka kaddamar a makon jiya an tabbatar da kashe manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram tare da sauran mabiyan kungiyar.
A cewar Enenche, da dama daga cikin mayakan sun samu raunuka wanda ba lallai ne su rayu ba, a lokacin da sojojin suka afka musu, ya kara da cewa, sojojin sun yi nasarar lalata kayayyakin mayakan da dama da suka hada da manyan bindigogi, babura, da kekuna.
Enenche ya ce, farmakin sojojin ya zo ne bayan wani yunkurin harin da bai yi nasara ba da mayakan na Boko Haram suka shirya kaiwa a mahadar garin Banki da jihar Borno. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China