Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Likitocin Najeriya sun bayar da gargadin shiga yajin aiki yayin da ake kokarin dakile COVID-19
2020-06-01 10:29:34        cri
Likitocin Najeriya sun bayar da sanarwar gargadin shiga yajin aiki muddin gwamnatin kasar ta gaza biya musu bukatunsu nan da kwanaki 14 masu zuwa, a yayin da kasar ke cigaba da yaki da annobar COVID-19.

Kungiyar likitoci ta Najeriya NARD, ta fadawa manema labarai cewa, ta cimma matsayar yanke shawarar shiga yajin aikin ne a ranar Asabar.

Sokomba Aliyu, shugaban kungiyar likitoci na kasar ya ce, batutuwan dake shafar tsarin kiwon lafiya da rayuwar ma'aikatan jinya su ne muhimman al'amurran dake gabansu.

Daga cikin bukatun da kungiyar ta NARD take nema daga wajen gwamnati sun hada da samar da isassun rigunan kariya ga jami'an lafiyar kasar, kamar kayayyakin taimakawa numfashi samfurin N95, da safar hannu, da sauran muhimman kayayyakin da jami'an lafiyar ke bukata wajen aikin yaki da annobar COVID-19, in ji Aliyu.

Likitocin suna kuma bukatar a dinga biyansu hakkokinsu a kan lokaci, kana a gaggauta dawo da takwarorinsu da aka sallama daga aikin a shiyyar tsakiyar Najeriya.

Likitocin sun yi kira ga jami'an tsaro musamman a jihohin Legas, Delta, da Abuja, da su dena cin zarafin likitocin a lokacin da suke gudanar da ayyukansu a yakin da ake da annobar COVID-19. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China