Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan bindiga sun kashe mutane 70 a arewa maso yammacin Najeriya
2020-05-29 10:46:44        cri
Kimanin mutane 70 aka yiwa jana'iza ta bai daya a ranar Alhamis wadanda suka mutu sanadiyyar hare haren da 'yan bindiga suka kaddamar a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda wasu majiyoyi da dama suka bayyana.

'Yan bindigar, wadanda aka tabbatar barayin shanu ne, sun kai adadin daruruwa haye a kan babura inda suka afkawa kauyukan Garki, Dan Aduwa, Kuzari, Katuma, da Masawa, dukkansu masu nisan kilomita 3 daga garin Sabon Birrnin Gobir dake jahar Sokoto a ranar Laraba.

Jami'an kiwon lafiya a asibitin gundumar Sabon Birni sun ce, adadin mutanen da suka mutu zai iya karuwa, kasancewar ma'aikatan dake aikin ceto suna cigaba da kaiwa gawarwakin mutanen da suka mutu da wadanda aka raunata a hare haren.

Hukumar 'yan sandan jahar ta ce, za ta yiwa manema labarai karin haske daga bisani, bayan tattara alkaluman barnar da 'yan bindigar suka haddasa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China