2020-06-01 16:02:24 cri |
Labari na hudu: Na yi kuka saboda tun farko ban shiga kungiyar yara ta kasar Sin ba
A duk lokacin da Xi jinping ya yi hira da yara,
Yana son ya saurari labaran da za su fada masa,
shi yana son fada musu,
labarinsa na yarinta.
Lokacin da ya ke karatu a makarantar firamare ta ungumar Haidian dake Beijing
yayin da ya halarci bikin shigar sabbin mambobin kungiyar yara ta kasar
ya fashe da kuka saboda tun farko bai samu damar shiga ba
Daga bisani kuma, lokacin da ya shiga kungiyar, hankalinsa ya tashi sosai
Lokacin da ya ga wani yaro ya rubuta kalmomin "Kara kokari don bautawa kasa",
Ya tuna cewa, yayin da yake shekaru 4 ko 5 a duniya
mahaifiyarsa ta saya masa wani littafi
dake bayani game da labarin Yue fei, jarumin al'ummun kasar Sin a zamanin da,
Ya tambayi mahaifiyarsa:
yin sassaka a baya akwai zafi?
Mahaifiyarsa ta ce:
Ko da yake akwai zafi, amma Yue Fei ba zai manta ba.
Xi Jinping ya fadawa yara cewa,
"kara kokari don bautawa kasa",
Har yau shi ma ba zai manta ba,
kuma zai dukufa kan wannan aiki a rayuwarsa.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China