Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban bankin Najeriya ya yi hasashen raguwar tattalin arzikin kasar a rubu'i na biyu na bana sakamakon annobar COVID-19
2020-05-29 12:49:49        cri
Babban bankin Najeriya CBN, ya yi hasashen raguwar karfin tattalin arzikin ma'aunin GDP na kasar a rubu'i na biyu na bana a sanadiyyar annobar COVID-19.

A cewar gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele, hada hadar tattalin arzikin 'yan Najeriya ta tsaya cik a yayin da ake yaki da cutar a kasar. Yana kyautata tsammanin za'a iya samun raguwar karfin tattalin arzikin kasar a cikin rubu'i na biyu na wannan shekarar da muka ciki.

Gwamnan ya fadawa 'yan jaridu cewa, Najeriya wani muhimmin ginshiki ne a tattalin arzikin duniya. Idan har kasar za ta iya jurewa wannan yanayi da ake ciki game da tasirin annobar cikin kankanin lokaci, kana za ta hada kai da sauran kasashen duniya domin fita daga matsanancin halin da ake ciki, hakika da hakan zai fi dacewa ga kasar.

Ya jaddada bukatar yin aiki tare domin cimma nasarar bunkasuwar tattalin arziki.(AHMAD)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China