Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Masu cutar COVID-19 a Afrika sun zarce 90,000
2020-05-21 10:29:34        cri

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika (Africa CDC), ta ce adadin mutanen da suka kamu da annobar COVID-19 a Afrika ya karu daga 88,172 a ranar Talata zuwa 91,598, ya zuwa yammacin Laraba.

Africa CDC, cibiyar kwararrun masana lafiyar kungiyar AU mai mambobin kasashe 55, ta sanar cikin alkalumanta na baya bayan nan cewa yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar COVID-19 a Afrika ya karu daga 2,835 a yammacin ranar Talata zuwa 2,912 a yammacin ranar Laraba.

Haka zalika cibiyar ta Africa CDC ta sanar cewa kimanin mutane 35,808 sun warke daga cutar COVID-19 a fadin nahiyar ya zuwa yammacin ranar Laraba, inda aka samu sabbin mutanen da suka warke daga cutar kimanin 2,002 cikin sa'o'i 24.

Alkaluman cibiyar Africa CDC ya nuna cewa, annobar ta yadu a dukkan fadin nahiyar, kasashen da annobar COVID-19 ta fi kamari a Afrika sun hada da Afrika ta kudu mai adadin mutane 17,200 da suka kamu da cutar, Masar tana da mutane 13,484, Algeria 7,377, yayin da kasar Morocco an samu mutane 7,023 sun kamu da cutar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China