2020-05-25 11:28:26 cri |
Jimillar adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar Afrika ya karu daga 103,933 a ranar Asabar zuwa mutane 107,412 ya zuwa safiyar ranar Lahadi, cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika, wato (Africa CDC) ta sanar da hakan a ranar Lahadi.
Hukumar dake yaki da annobar a nahiyar ta bayyana cewa, kawo yanzu, cutar ta riga ta yadu a kasashen Afrika 54, kana hukumar ta kara da cewa, ya zuwa safiyar Lahadi mutane 42,626 sun warke bayan kamuwa da cutar ta COVID-19.
A cewar Africa CDC, adadin mutanen da cutar COVID-19 ta kashe a fadin nahiyar Afrika ya karu daga 3,183 a safiyar ranar Asabar, zuwa mutane 3,246 a safiyar ranar Lahadi.
Cibiyar dakile yaduwar cutukan ta Afrika ta ce, shiyyar arewacin Afrika ne annobar COVID-19 ta fi yiwa illa a duk fadin nahiyar ta fuskar yawan adadin mutanen da suka kamu da cutar da kuma wadanda suka mutu a sanadiyyar cutar.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China