Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dukkan kasashen Afrika sun harbu da COVID-19 bayan rahoton farko na kamuwa da cutar a Lesotho
2020-05-14 10:32:35        cri
Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Lesotho a ranar Laraba ta tabbatar da samun rahoton farko na bullar annobar COVID-19, inda hakan ya tabbatar da kasa ta karshe da ta kamu da cutar a nahiyar Afrika.

Ma'aikatar ta sanar cewa ta gudanar da gwaje gwajen cutar COVID-19 kimanin 81 a ranar 9 ga watan Mayu ga mutanen da suka yi tafiye tafiye daga kasashen Afrika ta kudu da Saudiyya.

A cewar sanarwar, kasar ta tura samfurin zuwa kasar Afrika ta kudu bayan da sakamakon ya dawo a ranar 12 ga wata an samu mutum guda da ya kamu da cutar.

Ma'aikatan lafiyar Lesothon ta ce, za ta cigaba da tantancewa da kuma gwajin dukkan wadanda ake zargin sun kamu da cutar, sannan za ta cigaba da bibiyar gidajen mutanen da aka baiwa umarnin su killace kansu.

Kasar ta aika da samfuri 597 zuwa Afrika ta kudu domin yin gwaje gwaje.

Baki dayan adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afrika ya zarce 69,500, bisa ga bayanai na alkaluman baya bayan nan da cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika ta sanar a ranar Laraba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China