![]() |
|
2020-05-21 10:39:06 cri |
Rundunar sojojin kasar Burkina Faso ta ce ta yi nasarar kashe 'yan ta'adda 47 yayin wani samame da ta kaddamar a sansanoni biyu na 'yan ta'addan a ranar Talata a arewa maso yammacin lardin Kossi.
Harin na ba zata ya haifar da mummunar barna ga 'yan ta'addan, musamman kashe mayakansu 47 da lalata kayayyakin aiki masu yawa na 'yan ta'addan, kamar yadda rundunar ta sanar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce, harin shi ne na karshe da sojojin suka kaddamar a sansanonin biyu dake yankin Waribere, mai tazarar kilomita 40 daga babban birnin lardin Barani.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China