![]() |
|
2020-03-10 09:42:49 cri |
Ministan lafiyar kasar Burkina Faso Claudine Louge ya sanar a jiya Litinin a taron manema labarai cewa mutane biyu sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a karon farko a kasar.
A cewar Louge, mutanen biyu ma'aurata ne inda matar ta dawo daga kasar Faransa a kwanan nan. A yanzu haka an killace majinyatan a wani asibiti dake Ouagadougou, babban birnin kasar.
Mutum na uku wanda shi ne ya yi mu'amala da mutanen biyu da suka kamu da cutar ana ci gaba da bibiyarsa, a cewar ministan lafiyar. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China