Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar WFP ta godewa Sin bisa gudummawar hatsi da ta ba Zimbabwe
2020-05-16 16:09:27        cri

Hukumar samar da abinci ta MDD wato WFP, ta godewa kasar Sin bisa gudummawar hatsi da ta ba kasar Zimbabwe cikin gaggawa.

Hukumar WFP ta bayyana haka ne a jiya, inda ta ce kasar Zimbabwe tana fuskantar karancin abinci mafi tsanani da ba a gani ba cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata.

Kasar Sin ta samar da gudummawar hatsi ga jama'ar kasar Zimbabwe kimanin dubu 250 ta hannun hukumar WFP don biyan bukatunsu a wannan fanni, kafin yanayin damina mai zuwa. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China