Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Zimbabwe ya gana da tawagar jami'an lafiyar Sin da suka isa kasar sa
2020-05-13 10:41:45        cri

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya ce gogewar da kasar Sin ta samu a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, zai amfani kasar sa, a yakin da take yi na ganin bayan wannan annobar. Shugaba Mnangagwa, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, bayan ganawa da tawagar kwararru a fannin lafiya da kasar Sin ta tura kasar sa.

Tawagar ta isa birnin Harare fadar mulkin kasar ne a ranar Litinin, tana kuma kunshe da kwararrun likitoci 12, wadanda za su gabatarwa takwarorin aikin su na Zimbabwen dabaru, da kwarewar da suke da ita a fannin yaki da wannan cuta.

Har ila yau, tawagar ta isa kasar tare da kayayyakin tallafin kiwon lafiya, wadanda suka kunshi na'urar taimakawa numfashi, da sinadaran gwajin cutar, da marufen baki da hanci, da kuma rigunan kariya na jami'an lafiya.

A jawabin sa na maraba da zuwan tawagar a fadar gwamnati, shugaba Mnangagwa, ya ce ko shakka babu, kwararrun jami'an lafiyar kasar sa, za su amfana daga gogewar takwarorin su na Sin, da suka kai musu daukin yaki da COVID-19, cutar da tuni ta haifar da asarar rayuka, ta kuma gurgunta harkokin rayuwa a daukacin sassan duniya, ciki hadda Zimbabwe. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China