Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kasar Sin sun baiwa Zimbabwe taimakon kayayyakin kiwon lafiya
2020-04-22 13:37:44        cri

A jiya ne kamfanonin Huawei da Sichuan PD Times na kasar Sin, suka mika wa gidauniyar da Auxillian Mnangagwa uwar gidan shugaban kasar Zimbabwe ta kafa mai suna Angel of Hope taimamakon kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

A jawabinta yayin bikin mika kayayyakin Madam Mnangagwa, ta ce ta tuna da goyon bayan da kasar Sin ta baiwa kasar Zimbabwe a shekarun 1960, lokacin da kasar ke gwagwarmayar neman 'yanci. Ta ce, tana godewa da yadda kasar Sin ta tuna da kasarta, a wannan lokaci da kasar ke fama da cutar COVID-19.

Kayayyakin da kamfanonin biyu suka bayar, sun hada da abubuwan rufe baki da hanci da ma'aikatan lafiya ke amfani da shi guda 50,000, da rigunan kariya 510 da tabaran kariya dubu 1. Za dai a raba wadannan kayayyakin kiwon lafiya ne, ga ma'aikatan lafiya dake aikin yaki da annobar COVID-19 a kasar ta Zimbabwe.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China