![]() |
|
2020-05-13 19:19:31 cri |
Zhao Lijian wanda ya bayyana haka yau, ya ce, tuni dai wadannan tawagogi suka dawo gida kasar Sin jiya Talata, bayan kammala aikinsu a wadannan kasashe. Yana mai cewa, tun lokacin barkewar COVID-19 zuwa wannan lokaci, kasar Sin ta tura tawagogin ma'aikatan lafiya biyar zuwa Afirka, ta kuma shirya taruka ta kafar bidiyo kimanin 30 da masana daga kasashen na Afirka.
Yanzu haka, akwai sama da tawagogin ma'aikatan lafiya 40 dake aiki a kasashen na Afirka, inda suke gudanar da ayyukan ba da horo kimanin 400, da raba fasahohi da dabarun yaki da wannan annoba da Afirka da horas da sama da jami'an lafiyar nahiyar 20,000.
Zhao ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa da 'yan uwanta kasashen Afirka da ci gaba da taimakawa Afirka a yakin da take yi da COVID-19, za kuma su yi aiki tare har sai sun kai ga samun nasarar ganin bayan wannan annoba.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China