Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun likitocin Sin sun tashi zuwa Zimbabwe
2020-05-11 19:14:09        cri

Yau Litinin 11 ga wata da safe, bisa gayyatar da jamhuriyar kasar Zimbabwe ta yi mata, tawagar kwararrun likitoci 12 na gwamnatin kasar Sin ta tashi daga birnin Changsha na lardin Hunan zuwa Zimbabwe, domin taimakawa kasar wajen dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Kwararrun likitocin sun tashi ta jirgin sama ne tare da kayayyakin kiwon lafiya da gwamnatin lardin Hunan ta samar, da suka kunshi na'urar taimakawa numfashi, da na'urar gwajin cutar COVID-19, da babbar na'urar tantance zafin jiki, da marufin baki da hanci samfurin N95, da kayan ba da kariya da sauransu.

Da isar su Zimbabwe, kwararrun likitocin za su yi cudanya kan fasahohin kandagarkin annobar COVID-19 da takwaransu na kasar, tare kuma da samar musu horon da abin ya shafa, a sa'i daya kuma, za su ba da jagoranci da tallafi ga tawagogin likitocin kasar Sin dake aiki a kasashen dake makwabta da Zimbabwe ta kafar bidiyo.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China