![]() |
|
2020-05-11 20:55:35 cri |
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, shi ne ya bayyana haka, yayin taron manema labarai yau Litinin a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda ya kira sabbin dokokin da Amurka ta fitar a matsayin "rura wutar rikicin siyasa kan kafofin watsa labaran kasar Sin."
A makon da ya gabata ne, kasar Amurka ta fito da wata sabuwar doka, da ta takaita takardun iznin shiga kasar ga manema labarai na kasar Sin na tsawon kwanaki 90, da zabin neman kari, matakin da ya fara aiki Litinin din nan.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China