Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Zimbabwe ya godewa kasar Sin kan taimakon da ta ba ta wajen yaki da COVID-19
2020-03-19 20:14:51        cri
Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya godewa kasar Sin da sauran kasashe, kan taimakon da suka ba ta, yayin da ta ke shirya matakan yaki da cutar COVID-19.

Shugaban ya bayyana haka ne, yayin da yake jawabi a bikin kaddamar da matakan kasar na yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Ya ce, "ina son na yi na'am da taimakon da Jamhuriyar jama'ar kasar Sin da gwamnatin Burtaniya suka baiwa kasar Zimbabwe."

Rahotanni na cewa, kasar Sin ta dauki nauyin gyara da daga darajar cibiyar killace da jinyar wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ta Zimbabwe dake gudana a halin yanzu, asibitin Wilkins dake Harare, babban birnin kasar.

Haka kuma, kasar Sin ta tura tawagar ma'aikatan lafiya zuwa kasar, don horas da ma'aikatan lafiyar kasar kan matakan yaki da COVID-19. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China