Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci a aiwatar da sakamakon babban taron Berlin game da batun rikicin Libya
2020-02-13 10:48:51        cri
Wakilin kasar Sin a jiya Laraba ya bukaci a aiwatar da sakamakon da aka samu a babban taron da aka gudanar a watan da ya gabata a birnin Berlin game da batun rikicin Libya bayan da kwamitin sulhun MDD ya amince da shi.

Kwamitin sulhun MDDr ya amince da kudurin mai lamba 2510 bisa samun kuri'u 14 da suka nuna goyon baya ga sakamakon taron na Berlin. Kasar Rasha ce kadai ba ta kada kuri'ar amincewa da sakamakon ba. Inda ta kauracewa jefa kuri'ar.

Kasar Sin tana fatan dukkan bangarorin kasar Libya, da sauran shiyyoyin kasasshen duniya masu ruwa da tsaki, da al'ummar kasa da kasa, za su yi aiki tare wajen hanzartar aiwatar da sakamakon taron na Berlin, a cewar Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD wanda ya bayyana hakan bayan kuri'ar da aka kada a MDDr.

Game da wannan batu, ya kamata sakatariyar MDD ta kafa wani tsarin tabbatar da cikakken shugabanci wanda 'yan kasar Libyan za su gudanar da kan su, wanda zai biya bukatun dukkan bangarorin kasar, kuma zai takaita ikon rawar da kasashen ketare ke takawa cikin harkokin kasar, a cewar Wu.

Wu ya ce, yayin aiwatar da sakamakon babban taron na Berlin, da kudurin kwamitinn sulhun MDD, da bangaren kasa da kasa, tilas ne su yi taka tsantsan game da batun ayyukan ta'addanci a kasar Libya da kewayenta, kuma bangarorin su yi kokarin kawar da dukkan nau'ikan ayyukan ta'addanci a kasar, kana su yi kandagarkin kwararar mayakan 'yan ta'adda daga wasu kasashen ketare ta kan iyakokin kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China