Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kungiyar yawon shakatawa ta Najeriya: Babu wariyar launin fata a kasar Sin
2020-05-01 21:08:08        cri

A ranar Laraba da ta gabata, Jaridar "The Nation" ta Najeriya ta wallafa wani bayanin da Anrinle Ahmed Adekunle, shugaban kungiyar yawon shakatawa ta kasar Najeriya, ya rubuta, mai taken "Ainihin abin da ya faru game da maganar wai Sinawa na cin zarafin 'yan Najeriya". Cikin bayaninsa, mista Adekunle ya soki yadda wasu mutane suka kirkiro maganar, gami da kokarin yada hotunan bidiyo na karya a kafafen sada zumunta, haka kuma ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi kokarin fahimtar ainihin abun da ya faru, maimakon bari a yaudare su da karairayi.

Mista Adekunle ya ce, kasar Sin ta dauki tsauraran matakai don dakile yaduwar cutar COVID-19, haka kuma ba ta taba nuna bambanci ga Sinawa da baki 'yan kasashen waje a yayin da take aiwatar da matakan ba. A cewarsa, dole ne a yi kokarin martaba dokokin kasar Sin a fannin ba da izinin shiga kasa, gami da ka'idoji masu alaka da aikin hana yaduwar cuta, matukar ana bin doka, to, ba za a gamu da matsala yayin da ake ziyartar kasar Sin ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China