Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurkawa bakaken fata da na yankin Latin na cikin hadarin kamuwa da COVID-19
2020-04-11 16:47:36        cri

Fadar White House ta shugaban Amurka, ta ce kasar na samun nasara a yakin da take da cutar COVID-19, sai dai jami'ai sun ce, Amurkawa bakaken fata da na yankin Latin na cikin hadari.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a jiya, yayin jawabi na kullum kan yakin da ake da cutar, wanda aka watsa ta kafar talabijin cewa, yayin da ake tsaka da fargaba, alamu a bayyane suke cewa managartan matakan da aka dauka na ceton rayuka da dama.

Sai dai jami'an fadar White House din sun ce cutar na tasiri kan al'ummomi masu launin fata.

Babban likita mai kula da lafiyar al'ummar Amurka, Jerome Adams, wanda BaAmurke ne bakar fata, ya ce al'ummomi masu launin fata da dama kamar Amurkawa bakaken fata da 'yan Latin Amurka na da adadi mai yawa na masu fama da cututtukan Asma da hawan jinni da sukari.

Ya ce wadannan matsalolin lafiya na sanya su cikin hadarin kamuwa da COVID-19, inda ya ce al'ummomin masu launin fata na da yawan masu cututtukan dake kara hadarin kamuwa da cutar COVID-19 mai tsanani.

Sai dai, ya kara da cewa, ba batu ne na kwayoyin hallita ba, sai dai na yanayin zamatakewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China