Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana adawa da siyasantar da asalin kwayar cutar COVID-19
2020-04-27 20:26:18        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, yadda ake siyasantar da batun asalin kwayar cutar COVID-19, ya saba asalin tsarin binciken kimiyya, kana bai dace da kokarin da duniya ke yi na yaki da annobar ba.

Geng ya bayyana haka ne Litinin din, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa a taron manema labarai da aka saba shiryawa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, kan ko kasar Sin tana duba yiwuwar gudanar da bincike na kashin kanta game da asalin kwayar cutar, inda ya jaddada cewa, batun gano asalin kwayar cuta, batu ne na kimiyya wanda ya kamata a damka shi ga masana kimiyya da kwararru domin su yi nazari, ba wai wasu su rika shaci fadi game da asalin kwayar cutar ba.

Ya ce, a baya-bayan nan mutane da dama a Amurka na ta yin tambaya da nuna damuwa kan ko gwamnatin Amurka ta dauki matakan da suka dace a kan lokaci kan wannan annoba. Kasar Sin tana fatan Amurka, za ta mayar da hankali kan damuwar al'ummarta da na kasashen duniya a kan lokaci.

Geng Shuang ya ce, kasar Sin tana adawa da yadda wasu mutane a Amurka ke fakewa da batun COVID-19 wajen shafawa kasar Sin kashin kaji da ma illata muradun ta. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China