Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya ya yi kira ga Sin da Afrika da su kara hadin kai don yakar COVID 19
2020-04-22 11:19:24        cri

Wani masani dan Najeriya, Issa Aremu ya wallafa wani bayanin da ya rubuta a jaridar Daily Trust mai taken "Kada a manta da dangantakar Sin da Afrika lokacin da ake tsaka da cutar COVDI-19", inda ya jaddada cewa, yanzu jama'ar Najeriya na cikin muhimmin lokaci na yakar wannan mumunar cutar cikin hadin kai. Ya ce nuna shakku ko shafawa kasar Sin bakin fenti kan taimakon da ta bai wa Najeriya da kuma bata sunanta, ba mataki ne da ya dace ba. Sannan kuma ya yi kira ga daukacin al'ummar Najeriya da ta kawar da jita-jita don ingiza dangantakar Sin da Afrika zuwa gaba.

Bayanin ya nuna cewa, game da halin da 'yan Afrika ke ciki a lardin Guangzhou dangane da kandagarkin cutar COVID-19, ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama ya nuna cewa, rashin kyawun mu'ammala ce kadai matsalar da ake fuskanta a wurin. Kada a manta, dangantakar Sin da Afrika na da inganci cikin dogon lokaci, hadin kan bangarorin biyu abu ne da ba a iya canjawa cikin dangantakar kasashen biyu. Hadin kan bangarorin biyu ya kawo karshen mulkin mallaka a nahiyar da kawar da bambancin launin fata, har ma ya magance cutar Ebola, don haka hanya daya tilo da bangarorin biyu za su bi wajen kawo karshen COVID 19 ita ce hadin kansu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China