Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta shirya kwashe 'yan kasarta da suka makale a kasashen waje sakamakon COVID-19
2020-04-21 20:51:23        cri
Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, ya ce gwamnatin kasar ta shirya kwashe 'yan Najeriya da suka makale a kasashen waje, sakamakon barkewar cutar numfashi ta COVID-19.

Geoffrey Onyeama ya shaidawa manema labarai hakan jiya Litinin a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Ya ce an tsara fara kwashe 'yan kasar su sama da 2,000, wadanda suka nuna sha'awar komawa gida tun daga mako mai zuwa.

Ministan ya kara da cewa, gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan takardar fahimtar juna da wasu kamfanonin jiragen sama guda biyu, wadanda za su yi jigilar 'yan kasar cikin farashi mai rahusa. To sai dai ba a fayyace ko kamfanonin na cikin gida ne ko kuma na ketare ba.

Tun cikin watan Maris da ya gabata ne dai Najeriya ta rufe filayen jiragen saman ta, a wani mataki na dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 zuwa sassan kasar.

Mr. Onyeama ya ce, yayin da ake jigilar masu komawa gidan, za a rika mayar da mutane 200 a ko wane rukuni. Hakan a cewar sa, zai ba da damar tsugunar da wadanda aka dauko cikin sauki a wuraren da aka tanada domin killace masu komawa gidan, kasancewar babu isassun wurare da za a killace mutane masu yawa sosai a lokaci guda. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China