Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu dauke da COVID-19 a Afrika ta Kudu ya kai 2,415
2020-04-15 10:30:25        cri
Ministan lafiyar kasar Afrika ta Kudu Zweli Mkhize, ya ce baki daya mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar ya kai 2,415.

A bisa alkaluman baya bayan nan da ya fitar game da cutar ministan ya ce, hakan ya biyo bayan samun karin sabbin mutane 143 da suka kamu da cutar a ranar Litinin.

A wani cigaban kuma, kasar Afrika ta kudu ta karbi tallafin kayayyakin yaki da cutar COVID-19 wanda kasar Sin ta bayar, kamar yadda sashen hulda da kasa da kasa da hadin gwiwa na Afrika ta kudu ya tabbatar.

Kayayyakin sun isa kasar tun a daren Litinin ta filin jirgin saman kasa da kasa na Tambo dake Johannesburg, kuma ministan lafiyar kasar Mkhize da ministan hulda da kasa da kasa da hadin gwiwa na kasar Naledi Pandor ne suka karbi kayayyakin a ranar Talata.

A rahoton da kafar yada labaran kasar ta News24 ta watsa ya nuna cewa, kayayyakin tallafin da kasar ta Sin ta samar ya je ne a daidai lokacin da kayayyakin aikin lafiya da suka hada da safar hannu da abin rufe fuska na kasar Afrika ta Kudun ke daf da karewa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China