Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: ya kamata mu yi tunani kan batutuwa guda shida kafin mu soke matakan hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19
2020-04-14 13:11:59        cri
Jiya Litinin, babban sakataren hukumar kiwon lafiyar duniya ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana yayin taron manema labarai cewa, wasu kasashe suna tunanin soke matakan hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, kamar dokar zama a gida da sauransu.

To sai dai fa bisa fasahohin da aka samu, an ce, ya kamata a yi tunani kan batutuwa guda shida, kafin soke matakan hana yaduwar cutar numfashin ta COVID-19, wadannan abubuwa sun hada da, tabbatar an riga an shawo kan yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma kafa tsarin kiwon lafiya dake iya ba da ikon ganowa, da bincike, da killacewa, da ba da jinya ga kowane mai dauke da cutar, da kuma nemo wadanda suka taba cudanya da masu dauke da cutar, da kawar da kalubalen barkewar annobar cikin asibitocin ba da jinya, da sauran wurare na musamman, da daukar matakan yin kandagarki, da hana yaduwar cutar a wuraren aiki, da makarantu, da sauran wuraren da ya kamata mutane su je.

Sauran matakan sun hada da gudanar da aikin sa ido kan wadanda suka shiga kasa daga kasashen ketare yadda ya kamata, da kuma sabawa da "sabon salon zaman rayuwa" bayan barkewar cutar.

Haka kuma, ya ba da shawarar cewa, ya kamata kowace kasa ta dauki matakai bisa dukkan fannoni, domin magance yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma ceton rayukan mutane, ta yadda za a dakile yaduwar cutar gaba daya. A sa'i daya kuma, ya ce, ya kamata mu ba da taimakon kiwon lafiya ga mutane masu karamin karfi, domin samun daidaituwar kayayyakin jinya, a lokacin da ake ba da jinya ga masu fama da cutar numfashi ta COVID-19, da masu dauke da sauran cututtuka. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China