![]() |
|
2020-04-13 12:28:03 cri |
A kokarinta na tunkarar tasirin annobar kan tattalin arziki, Tarayyar Afrika (AU) ta nada wasu wakilai na musammam da za su kula da batun tallafin kasashen duniya ga nahiyar.
Ana ganin akwai yiyuwar tsarukan kiwon lafiya a nahiyar da suka tabarbare za su ci gaba da fuskantar gagagrumar matsala, musammam a yankunan karkara. A don haka, hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga kasashen Afrika su dauki matakan gaggawa na karfafa tsarukan kiwon lafiyar al'umma da na kiwon lafiya a matakin farko, inda kuma ta yi kira ga kungiyar G20 ta gaggauta tallafawa nahiyar a kokarinta na yaki da cutar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China