Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An hana tafiye-tafiye tsakanin biranen Sudan yayin da ake fama da bazuwar COVID-19
2020-04-13 10:40:26        cri
Gwamnatin Sudan ta yanke shawarar hana tafiye-tafiyen motocin haya tsakanin biranen kasar, da nufin dakile yaduwar cutar COVID-19.

Baya ga haka, Firaministan kasar Abdalla Hamdok, ya fitar da wani umarni na gaggawa da ya tanadi hukunci ga wadanda suka keta matakan kebe kai, ko cin zarafin ma'aikatan lafiya ko kuma kawo tsaiko ga aikin jinya.

Kawo yanzu, rahoton ma'aikatar lafiya ta kasar, ya tabbatar da mutane 19 sun kamu da cutar, ciki har da mutane 2 da suka mutu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China