Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai bukatar nuna halin ya kamata yayin dakile annobar COVID-19
2020-04-03 20:45:20        cri
A yau Jumma'a a nan birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, akwai bukatar a nuna sanin ya kamata yayin da ake kokarin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Rahotanni sun nuna cewa, jiya mujallar The Diplomat ta wallafa wata budaddiyar wasikar da masanan kasar Sin 100 suka rubuta wa bangarori daban daban na Amurka, inda aka yi kira cewa, ya dace a kara karfafa hadin kai tsakanin kasa da kasa domin cimma burin kafa kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adam

Yayin taron ganawa da manema labarai da aka saba yi, madam Hua ta bayyana cewa, ta ga tuni wasu shugabannin kasashen duniya sun ba da amsa ga wasikar.

Madam Hua ta ce, "Kamar sauran kasashen duniya, kasar Sin ita ma tana fama da tasirin da kwayar cutar COVID-19 ke haifar mata, a don haka ya dace al'ummomin kasashen duniya su hada kai domin ganin bayanta nan da nan, ta yadda za a kare lafiyar daukacin bil Adama. Kasar Sin tana maraba kuma tana fatan kasashen duniya, musamman ma kasar Amurka za ta gabatar da ra'ayoyin da hankali zai dauka."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China