Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta yi zaman makoki a ranar 4 ga watan Afrilu a duk fadin kasar
2020-04-03 13:12:20        cri

Yau Jumma'a majalisar gudanarwar kasar Sin ta sanar da cewa, za a yi zaman makoki gobe Asabar, ranar 4 ga watan Afrilu a duk fadin kasar, da zummar nuna ta'aziyya ga jaruman da suka sadaukatar da rayukansu, wajen yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da annobar.

A dai goben kuma, za a saukar da tuta zuwa rabin sanda a duk fadin kasar Sin, da kuma ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen ketare. Za a dakatar da dukkan harkokin nishadi a kasar. Kuma daga karfe 10 na safen goben, al'ummar kasar Sin za ta yi shiru na mintuna 3, a matsayin nuna jimami, yayin da motoci, da jiragen kasa, da jiragen ruwa za su yi hon, kana za a kunna jiniyar gargadi. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China