Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Sin sun raba fasahar yakar COVID-19 da kasashen Asiya da Turai
2020-04-03 14:36:00        cri

Yammacin jiya Alhamis, masana 7 dake aikin yakar COVID-19 daga asibiti na farko karkashin jami'ar kimiyya da fasaha ta kasar Sin, sun yi tattaunawa da takwarorinsu na asibitoci fiye da 70 na kasashen Indiya, da Pakistan, da kuma Poland, kana da Switzerland, da Jamus da Birtaniya, da kuma Rasha ta kan Intanet kan aikin yakar cutar.

Yayin tattaunawar tasu, masanan kasar Sin sun raba fasahohin ba da jiyya ga masu fama da cutar, tare da gabatar da tsari na musamman da jami'ar ta fitar, wadda ta yi amfani da sinadarin magunguna na mAb wato Tocilizumab, da kuma ci gaban da suka samu a wannan fanni. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China